41 Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.
42 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi,
43 har suka ɗauki kwando goma sha biyu cike da gutsattsarin gurasar da na kifin.
44 Waɗanda suka ci gurasan nan kuwa maza dubu biyar ne.
45 Nan da nan ya sa almajiransa su shiga jirgi su riga shi hayewa zuwa Betsaida, kafin ya sallami taron.
46 Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu'a.
47 Da magariba ta yi, jirgin na tsakiyar teku, Yesu kuwa na nan kan tudu shi kaɗai,