51 Sa'an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai,
52 don ba su fahimci al'amarin gurasan nan ba, saboda zuciyarsu ta taurare.
53 Da suka haye, suka isa ƙasar Janisarata, suka ɗaure jirgin a gaɓa.
54 Da fitarsu daga jirgin sai mutane suka shaida shi.
55 Suka gama ƙasar da gudu, suka fara ɗaɗɗauko marasa lafiya a kan shimfiɗunsu zuwa duk inda suka ji yake.
56 Duk inda ya shiga kuma, birni ko ƙauye ko karkara, sukan kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa, su roƙe shi su taɓa ko ma da gezar mayafinsa ma. Iyakar waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.