16 Duk mai kunnen ji, yă ji.]”
17 Bayan rabuwarsa da taron, da ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi ma'anar misalin.
18 Ya ce musu, “Ashe, ku ma ba ku da fahimta ne? Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum daga waje, ba yadda zai ƙazanta shi,
19 tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.
20 Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazanta shi.
21 Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina,
22 da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.