25 Nan da nan sai wata mace, wadda 'ya tata ƙarama take da baƙin aljan ta ji labarinsa, ta zo ta fāɗi a gabansa.
26 Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa 'ya tata da aljanin.
27 Yesu ya ce mata, “Bari 'ya'ya su ƙoshi tukuna, domin bai kyautu a bai wa karnuka abincinsu ba.”
28 Amma ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”
29 Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.”
30 Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
31 Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.