28 Amma ta amsa masa ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”
29 Sai ya ce mata, “Saboda wannan magana taki, koma gida, aljanin, ai, ya rabu da 'yarki.”
30 Sai ta koma gida ta iske yarinyar a kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
31 Sai ya komo daga wajen Taya, ya bi ta Sidon ya je Tekun Galili ta Dikafolis.
32 Suka kawo masa wani kurma mai i'ina, suka roƙe shi ya ɗora masa hannu.
33 Yesu ya ɗauke shi suka koma waje ɗaya, rabe da taron, ya sa yatsotsinsa a kunnuwansa, ya tofar da yau, ya kuma taɓa harshensa.
34 Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”