1 Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.
2 Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu ya haifi Yahuza da 'yan'uwansa,
3 Yahuza kuwa ya haifi Feresa da Zera (uwa tasu Tamar ce), Feresa ya haifi Hesruna, Hesruna ya haifi Aram,
4 Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
5 Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,