4 Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
5 Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,
6 Yesse ya haifi sarki Dawuda.Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),
7 Sulemanu ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,
8 Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Azariya,
9 Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,
10 Hezekiya ya haifi Manassa, Manassa ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya.