32 “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.
33 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”
34 “Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.
35 Domin na zo ne in haɗa mutum da ubansa gāba, 'ya da uwatata, matar ɗa kuma da surukarta.
36 Zai zamana kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa.
37 Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
38 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.