13 Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan.
14 Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
15 Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.
16 Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.
17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
18 “Ga barana wanda na zaɓa!Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.
19 Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba,Ba kuma wanda zai ji muryarsa tasa a titi.