14 Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
15 Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.
16 Sai ya kwaɓe su, kada su bayyana shi.
17 Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,
18 “Ga barana wanda na zaɓa!Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai.Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.
19 Ba zai yi husuma ko magana sama sama ba,Ba kuma wanda zai ji muryarsa tasa a titi.
20 Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba,Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,Har ya sa gaskiya ta ci nasara.