6 Ina dai gaya muku, ga wanda ya fi Haikali a nan.
7 Da kun san ma'anar wannan cewa, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba’, da ba ku ga laifin marasa laifi ba.
8 Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”
9 Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu.
10 Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne.
11 Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba?
12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.”