9 Sai ya ci gaba daga nan ya shiga majami'arsu.
10 Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne.
11 Ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da tunkiya, ta faɗa a rami ran Asabar, ba zai kama ta ya fitar da ita ba?
12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja? Domin haka ya halatta a yi alheri a ran Asabar.”
13 Sa'an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa. Sai ya koma lafiyayye kamar ɗayan.
14 Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.
15 Da Yesu ya gane haka, ya tashi daga nan. Sai jama'a da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su duka.