12 Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
13 Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.
14 Lalle a kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,‘Za ku ji kam, amma ba za ku fahimta ba faufau,Za ku kuma gani, amma ba za ku gane ba faufau,
15 Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta,Sun toshe kunnuwansu,Sun kuma runtse idanunsu,Don kada su gani da idanunsu,Su kuma ji da kunnuwansu,Su kuma fahimta a zuciyarsu,Har su juyo gare ni in warkar da su.’
16 Albarka tā tabbata ga idanunku domin suna gani, da kuma kunnuwanku domin suna ji.
17 Hakika, ina gaya muku, annabawa da adalai da yawa sun yi ɗokin ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.
18 “To, ga ma'anar misalin mai shukar nan.