55 Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?
56 'Yan'uwansa mata ba duk tare da mu suke ba? To a ina ne mutumin nan ya sami waɗannan abu duka?”
57 Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”
58 Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.