33 Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”
34 Da suka haye, suka sauka a ƙasar Janisarata.
35 Da mutanen garin suka shaida shi, sai suka aika ko'ina a duk karkarar, aka kakkawo masa dukan marasa lafiya,
36 suka roƙe shi su taɓa ko da gezar mayafinsa ma, iyakar waɗanda suka taɓa kuwa suka warke.