6 To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,
7 har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa.
8 Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”
9 Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.
10 Ya aika aka fille wa Yahaya kai a kurkuku,
11 aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwa tasa.
12 Almajiransa suka zo suka ɗauki gangar jikin, suka binne, suka kuma je suka gaya wa Yesu.