1 Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce,
2 “Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”
3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku?
4 Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’