2 “Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”
3 Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku?
4 Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’
5 Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’
6 Wato, saboda al'adunku kun bazanta Maganar Allah.
7 Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,
8 ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni,Amma a zuci nesa suke da ni.