27 Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”
28 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.
29 Yesu ya tashi daga nan, ya bi ta bakin Tekun Galili. Sai ya hau dutse ya zauna a can.
30 Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su.
31 Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.
32 Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”
33 Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”