18 Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.
19 Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.”
20 Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.
21 Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
22 Sai Bitrus ya ja shi waje ɗaya, ya fara tsawata masa, ya ce, “Allah ya sawwaƙe, ya Ubangiji! Wannan har abada ba zai same ka ba!”
23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”
24 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.