23 za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.
24 Da suka zo Kafarnahum masu karɓar rabin shekel na gudunmawar Haikali suka je wurin Bitrus, suka ce, “Malaminku yana ba da gudunmawar?”
25 Ya ce, “I, yakan bayar.” Da ya dawo gida kuma, sai Yesu ya fara yi masa magana ya ce, “Me ka gani, Bitrus? Wurin wa sarakunan duniya suke karɓar kuɗin fito ko haraji, a wurin 'ya'yansu, ko kuwa daga wurin waɗansu?”
26 Sa'ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, 'ya'yan an ɗauke musu ke nan.
27 Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”