1 Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,
2 “Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.”
3 Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.
4 Sai ya tara dukan manyan firistoci da malaman Attaura na jama'a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu.
5 Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, ta ƙasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta cewa,
6 ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza,Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba,Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki,Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”