1 “Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.
2 Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa.
3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa.
4 Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.
5 Da ya sāke fita wajen tsakar rana, da kuma azahar, ya sāke yin haka dai.