2 Da ya yi lada da su a kan dinari guda a yini, sai ya tura su garkarsa.
3 Wajen ƙarfe tara kuma da ya fita, sai ya ga waɗansu suna zaman banza a bakin kasuwa.
4 Sai ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata, zan kuwa biya ku abin da yake daidai.’ Sai suka tafi.
5 Da ya sāke fita wajen tsakar rana, da kuma azahar, ya sāke yin haka dai.
6 Wajen la'asar kuma ya fita ya sami waɗansu a tsaitsaye, ya ce musu, ‘Don me kuke zaman banza yini zubur?’
7 Sai suka ce masa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata.’
8 Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’