1 Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,
2 ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su.
3 Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”
4 An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
5 “Ku ce wa 'yar Sihiyona,Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,Mai tawali'u ne,Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6 Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu.