34 Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar.
35 Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya.
36 Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka.
37 Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’
38 Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’
39 Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.
40 To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?”