43 Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.
44 Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake.
46 Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.