25 To, an yi waɗansu 'yan'uwa maza bakwai a cikinmu. Na farkon ya yi aure, da ya rasu, da yake bai haifu kuma ba, sai ya bar wa ɗan'uwansa matarsa.
26 Haka ya faru ga na biyun da na ukun, har ya kai kan na bakwai ɗin.
27 Bayansu duka sai matar ta rasu.
28 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu, su bakwai ɗin? Don duk sun aure ta.”
29 Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.
30 Domin a tashin matattu, ba a aure, ba a aurarwa, sai dai kamar mala'ikun da suke Sama ake.
31 Game da tashin matattu, ashe, ba ku taɓa karanta abin da Allah ya ce muku ba? cewa,