36 “Malam, wane umarni ne mafi girma a cikin Attaura?”
37 Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.
38 Wannan shi ne babban umarni na farko.
39 Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’
40 A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”
41 Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya,
42 ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”