8 Sa'an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin fa ya shiryu sosai, amma waɗanda aka gayyata ba su cancanta ba.
9 Saboda haka ku tafi ƙofofin gari, ku gayyato duk waɗanda kuka samu, su zo bikin.’
10 Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.
11 “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba.
12 Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.
13 Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’
14 Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”