1 Sa'an nan Yesu ya yi wa jama'a da almajiransa magana, ya ce,
2 “Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.
3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.
4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.
5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.
6 Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u,