3 Don haka, sai ku kiyaye, ku kuma aikata duk abin da suka gaya muku, amma banda aikinsu. Don suna faɗa ne, ba aikatawa.
4 Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.
5 Duk ayyukansu suna yi ne don idon mutane, suna yin layunsu fantam-fantam, lafin rigunansu kuma har gwiwa.
6 Suna son mazaunan alfarma a wurin biki, da mafifitan mazaunai a majami'u,
7 a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.
8 Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.
9 Kada ku kira kowa ‘Uba’ a duniya, domin Uba ɗaya ne yake gare ku, wanda yake cikin Sama.