40 A sa'an nan za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
41 Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
42 To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.
43 Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.
44 Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”
45 “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?
46 Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.