45 “Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?
46 Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.
47 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.
48 Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’
49 sa'an nan ya soma dūkan abokan bautarsa, yana ci yana sha tare da mashaya,
50 ai, ubangidan wannan bawa zai zo a ranar da bai zata ba, a kuma lokacin da bai sani ba,
51 yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”