1 “Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.
2 Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuwa masu hikima.
3 Don kuwa a lokacin da wawayen nan suka ɗauki fitilunsu, ashe, ba su riƙo mai ba.
4 Masu hikimar nan kuwa sun riƙo kwalaben mai da fitilunsu.
5 Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.
6 Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’