13 Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”
14 “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.
15 Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi.
16 Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.
17 Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri.
18 Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa.
19 To, da aka daɗe sai ubangijin bayin nan ya dawo ya daidaita lissafi da su.