27 Ya kamata ka sa kuɗina a ma'aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba!
28 Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.
29 Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”
31 “Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.
32 Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.
33 Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.