10 suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”
11 To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”
12 Amma da manyan firistoci da shugabanni suka kai ƙararrakinsa, bai ce kome ba.
13 Sai Bilatus ya ce masa, “Ba ka ji yawan maganganun da suke ba da shaida a kanka ba?”
14 Amma bai ba shi wata amsa, ko da ta kalma ɗaya ba, har mai mulki ya yi mamaki ƙwarai.
15 To, a lokacin idi kuwa mai mulki ya saba sakar wa jama'a kowane ɗaurarre guda da suka so.
16 A lokacin kuwa da wani shahararren ɗan sarƙa, mai suna Barabbas.