3 Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan,
4 ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”
5 Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.
6 Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.”
7 Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi.
8 Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini.
9 Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima,