4 ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”
5 Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.
6 Amma manyan firistoci suka tsince kuɗin suka ce, “Bai halatta mu zuba su a Baitulmalin Haikali ba, don kuɗin ladan kisankai ne.”
7 Sai suka yi shawara, suka sayi filin maginin tukwane da kuɗin don makabartar baƙi.
8 Don haka, har ya zuwa yau, ana kiran filin nan filin jini.
9 Ta haka aka cika faɗar Annabi Irmiya cewa, “Sun ɗauki kuɗin azurfa talatin ɗin nan, wato, awalajar shi wannan da waɗansu Isra'ilawa suka yi wa kima,
10 suka sayi filin maginin tukwane da su, yadda Ubangiji ya umurce ni.”