12 Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka,
13 suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci.
14 In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.”
15 Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.
16 To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.
17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
18 Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.