17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
18 Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.
19 Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,
20 kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”