1 Sa'an nan sai Ruhu ya kai Yesu cikin jeji, domin Iblis yă gwada shi.
2 Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.
3 Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”
4 Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa,‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba,Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”
5 Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,
6 ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, to dira ƙasa. Don a rubuce yake cewa,‘Zai yi wa mala'ikunsa umarni game da kai,’da kuma‘Za su tallafe ka,Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”