11 Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.
12 To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.
13 Ya kuma bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin teku, a kan iyakar ƙasar Zabaluna da Naftali,
14 domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,
15 “Ƙasar Zabaluna da ƙasar Naftali,Da bakin bahar, da hayin Kogin Urdun,Da kuma ƙasar Galili ta al'ummai,
16 Mazaunan duhu sun ga babban haske,Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta,Haske ya keto musu.”
17 Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”