1 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku.
2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.
3 Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?
4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?