13 “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.
14 Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”
15 “Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.
16 Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?
17 Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya.
18 Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan 'ya'ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan 'ya'ya.
19 Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.