19 Sai wani malamin Attaura ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.”
20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”
21 Sai ɗaya daga almajiran ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”
22 Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”
23 Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.
24 Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.
25 Sai almajiransa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ya Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!”