1 Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,
2 duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil'azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,
3 ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa'azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,
4 zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka.Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.
5 Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al'amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,
6 sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda 'ya'yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha'a ko na kangara.