1 Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.
2 Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah.
3 Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.
4 Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.