5 Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.
6 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.
7 Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.
8 Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.
9 Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.
10 Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.
11 Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.